Majiyoyi na cewa a cikin mota aka dasa Bam din da ya tashi ya kashe mutane da yawa da jikkata wasu mutane da dama.
Wadanda suka ga harin sunce yawanci fararen hula ne suka mutu ko suka jikkata.
Masu aikin agaji sunce yawan mamata na iya karuwa saboda yadda aka sami wasu da raunuka masu tsanani.
A halin da ake ciki shugaban kasar Bashar al-Assad ya ce yana shirye domin a tattauna dashi don kawo karshen yakin kasar muddin dai ‘yan ta'adda ba zasu yi amfani da damar wajen alfahari ba, kuma da fatan masu taimakawa ‘yan tawayen za su daina.288